Posts

Showing posts with the label BAHAUSHE

BAHAUSHE KO BAFILATANI?Ali Abubakar Sadiq

Image
Bahaushe ya ce sai an kula kashi ya ke doyi....ina kira da babbar murya ga matasan Arewa ku rabu da duk wadanda ke kokarin kunna wutar fitina tsakanin Hausawa da Fulani. Duk musulmi da ya ci sunan musulmi, wallahi ya girmi kabilanci. Babban abinda musulunci ya zo yayi yaki da shi a Doron kasa bayan shirka, bai wuce kabilanci ba. Sannan musulunci ya na yakar zalunci daga duk inda ya fito, ko a cikin gidanku ne. Duk al'ummar da ta gina tunanin yayanta kan kabilanci (kamar mu a nan Najeriya) wallahi har abada ba za ta kai gaci ba.  Ka gama zagin bahaushe ko bafilatani, ka na matsawa kadan sai dan Birom ko wata kabilar Middle Belt ya far maka. Shi kuma Dan Middle Belt da ya haura river Niger ko Benue sai Dan kudu ya far masa a matsayinsa na Dan Arewa. Shi kuma inyamurin kudu ya far wa duk yanuwansa na kudu. Yan Nigeria Delta su far wa Inyamuri yayin da Yarbawa su ke far wa kowa. Duk mai bibiyar tarihin Najeriya da idon basira zai gane cewa da gangan turawan mulk...