BAHAUSHE KO BAFILATANI?Ali Abubakar Sadiq
Bahaushe ya ce sai an kula kashi ya ke doyi....ina kira da babbar murya ga matasan Arewa ku rabu da duk wadanda ke kokarin kunna wutar fitina tsakanin Hausawa da Fulani. Duk musulmi da ya ci sunan musulmi, wallahi ya girmi kabilanci. Babban abinda musulunci ya zo yayi yaki da shi a Doron kasa bayan shirka, bai wuce kabilanci ba. Sannan musulunci ya na yakar zalunci daga duk inda ya fito, ko a cikin gidanku ne. Duk al'ummar da ta gina tunanin yayanta kan kabilanci (kamar mu a nan Najeriya) wallahi har abada ba za ta kai gaci ba.
Ka gama zagin bahaushe ko bafilatani, ka na matsawa kadan sai dan Birom ko wata kabilar Middle Belt ya far maka. Shi kuma Dan Middle Belt da ya haura river Niger ko Benue sai Dan kudu ya far masa a matsayinsa na Dan Arewa. Shi kuma inyamurin kudu ya far wa duk yanuwansa na kudu. Yan Nigeria Delta su far wa Inyamuri yayin da Yarbawa su ke far wa kowa.
Duk mai bibiyar tarihin Najeriya da idon basira zai gane cewa da gangan turawan mulki su ka dunkule mu waje guda da masaniyar cewa banbanci kabila, addini da yanayi ba zai taba bamu damar aiki tare ba. Daga samun yancin kai mun ga yadda murhu uku na Arewa, yamma da gabas, karkashin jagoranci na kabilanci inda Sardauna, Awolowo da Zik kowannensu ya tafi a kan siyasar kabilanci.
Mun ga yadda kabilancin ya Haifar da yaki mafi muni a Afirka, wato yakin Biafra wanda ya lakume rayuka kusan miliyan biyu a banza a wofi. Mun ga yadda juye-juyen mulkin sojoji a doron kabilanci ya tauye ci gaba da Najeriya zata samu. Mun ga yadda hatta siyasa da jam'iyyun siyasa aka gina su kan kabilanci. A shekaru 60 na wanzuwar kasar me kabilanci ya Haifar mana?
Ku na zaton a banza aka samar da kalmar Hausa-Fulani? Ba don wannan haduwa ba, bayan tafiyar turawa, da sai Hausawa da Fulani sun zama bayin Yan kudu a wannan kasar kamar yadda turawa su ka bautar da mu. Amma haduwar manyan Hausawa da Fulani shine abinda ya ba mu damar zama jigon mulki a Najeriya, sai dai Kash! Duk da kaucewa bautar Yan kudu mun zama bayin manyan mu (elites) na Arewa wadanda maimakon gina mu, sun gina yayansu da makusantansu ne kawai. Sakamakon tarbiyar nepotism da su ka gada wajen su Sardauna, wadda ita kuma wannan halayya ta nepotism ta Haifar mana da kwarafshin wadda ta kassara Arewa. A yanzu yakin da ke gabanmu ba na Hausawa da Fulani ba ne, ya ki ne na nemo wa Hausawa da Fulani yancinsu a Arewa.
Babban abin takaici shine dakikancinmu da wautar mu, na kasa amfani da basira wajen kwaikwayon elites din mu na Najeriya, wadanda a Lagos ko Abuja, ba ruwansu da wani kabilanci, addini ko bangaranci. Bahaushe, Bayarabe da Igbo ko kananan kabilu, a sama, zaka samu kabilarsu ita ce "Najeriya", addininsu Kuma shine "Wasoson arzikinmu" bangaranci su kuma bai wuce "kare junansu" daga mu ba.
Kai wawan matashi, Dan Arewa, wanda yankin ka ke cikin kuncin talauci, jahilci, rashin aiki da rashin tsaro, shin ka na kokarin ka zauna kana rura sabuwar wuta da zata karasa kone ka kurmus ne? Wallahi babu dabbancin da ya kai haka. Matasa ku farka ku kwato kanku daga bauta da elites din Arewa su ka kakaba muku, maimakon ku ci gaba da rura wutar bautar da tunaninku da rayuwarku. Ku sani, wallahi duk wanda yayi imani da Allah, musulmi ko kirista, to rungumar aikin kabilanci daidai ya ke da kafircewa Qurani da Attaura da linjila. Ku hade waje guda wajen yakar duk wani irin zalunci da za'a yi wa bahaushe ko bafilatani, Birom ko Bachama, musulmi ko kirista, Dan Arewa ko Dan kudu. Ta haka kadai za ku yanta tunaninku da rayuwarku.
Wanda bai ji bari ba, zai ji woho!!!
Comments
Post a Comment
Northern Nigeria Perspective is welcoming all comments, observations or views. The use of foul/vulgar language, pornographic materials and such other inappropriate comments are not allowed