Posts

Showing posts with the label QUR’ANI...IN

KURA-KURAI GOMA NA KIMIYYA A QUR’ANI...IN JI MULHIDAIAli Abubakar Sadiq

Image
A baya bayan nan Mulhidai, Riddaddu da makiya Musulunci sun shigo da wata sabuwar hanya ta sukar addinin musulunci, musamman a kasashen yamma, ta amfani da cewa akwai tarin kura-kurai na kimiyya a cikinsa. Na sha gwagwarmaya da irin wadannan mutane a dandalin Quora inda na kalubalanci duk wani mai wannan da’awar ya kawo duk wani abu da yake tsammani na kimiyya ne wanda ya ci karo, ko ya sha banban da Qur’ani. Dalili na kuwa bai wuce cewa na yi imani da cewa Allah dai shine wanda ya yi duk wata halitta, kuma a tsari irin na kimiyya ya yi halittunsa, sannan shine wanda ya saukar da Qur’ani, don haka duk wanda ya ce akwai karo daga wadannan bangarori guda biyu, to tabbas bai wuce ko dai ba shi da ilimin Qur’ani yadda ya kamata, ko kuma ba shi da ilimin kimiyya cikakke.  Abokan muhawara ta sun kalubalance ni da kawo tambayoyi guda goma da su ka jibanci kimiyya a Qur’ani wadanda su ka hada da;  1.Samar da maniyya a jikin dan Adam (Sperm factory) 2. Halittar mutum daga g...