MENENE ABIN BURGEWA A CIKI?Ali Abubakar Sadiq

Hoton Gwamnan Kano da wasu Yara biyu da aka tsinto su na kwana a titi ya karade social media. Yawancin mutane na ta yabawa wannan kokari na Gwamna, amma menene abin burgewa a ciki? Ga duk mai shekaru irin namu, ya san cewa wannan dabi'ar sabuwa ce ta zamani, domin a shekarun baya babu wanda zaka samu ya na kwana a titi face mahaukata ko yan kwaya. Amma duk wani mutum komai rashin gatansa ya na da inda ya ke kwana. A unguwanni zaka sami soraye manya da ke zama wajen kwanan almajirai da baki wani lokaci ma har masallatai na karbar bakuncin baki. Bahaushe na da hadisinsa cewa "Da, na kowa ne" don haka babu yadda za a yi kaga wani mai karamin shekaru ya kwana a titi, ko manya sai dai wadanda su ka fada ajin mahaukata ko yan kwaya. To amma yanzu Allah kadai ya san yawan mutane manya da yara da ke kwana a titi. Me ya jawo haka? Idan na takaita a kan yara masu kwana a titi, dalilai suna da yawa, kama da mummunar dabi'ar bara wadda malamai da iyayen zamani su ka assasa wadda ...