MENENE ABIN BURGEWA A CIKI?Ali Abubakar Sadiq
Hoton Gwamnan Kano da wasu Yara biyu da aka tsinto su na kwana a titi ya karade social media. Yawancin mutane na ta yabawa wannan kokari na Gwamna, amma menene abin burgewa a ciki? Ga duk mai shekaru irin namu, ya san cewa wannan dabi'ar sabuwa ce ta zamani, domin a shekarun baya babu wanda zaka samu ya na kwana a titi face mahaukata ko yan kwaya. Amma duk wani mutum komai rashin gatansa ya na da inda ya ke kwana. A unguwanni zaka sami soraye manya da ke zama wajen kwanan almajirai da baki wani lokaci ma har masallatai na karbar bakuncin baki.
Bahaushe na da hadisinsa cewa "Da, na kowa ne" don haka babu yadda za a yi kaga wani mai karamin shekaru ya kwana a titi, ko manya sai dai wadanda su ka fada ajin mahaukata ko yan kwaya. To amma yanzu Allah kadai ya san yawan mutane manya da yara da ke kwana a titi. Me ya jawo haka?
Idan na takaita a kan yara masu kwana a titi, dalilai suna da yawa, kama da mummunar dabi'ar bara wadda malamai da iyayen zamani su ka assasa wadda a baya ba haka abin yake ba. Wato a da zaka samu duk wanda za'a tura bara wani gari, zaka tarar shekarunsa sun isa ya yi noma, wato daga sha biyu abinda yayi sama, sabanin yanzu da zaka ga yara Yan shekaru hudu ko biyar. Iyaye su na son su yi ta aure su na haihuwa amma ba sa son daukar dawainiyar Yayansu. Malamai na son su tara dalibai birjik domin samun kudade hannun iyaye, samun sadaka da wadanda za su yi musu hidima ta aiki ko noma. Don haka iyaye ke watsawa malamai nauyinsu, su kuma malamai su watsowa al'umma.
Dalilin wannan tabi'a, tare da waccan halayya ta haihuwa barkatai, ya sa Arewacin Najeriya ta zama headquarter yaran da ake kira "out of school children" wanda a yanzu kididdiga ke nuna cewa sun kai miliyan 15.3, inda Arewa maso yamma ke da miliyan 5 sannan Kano ke zama ja-gaba da sama da miliyan 1.
To don Allah don Gwamna ya tsakuro yara biyu har wani abin yamadidi ne? Na farko dai a matsayinsa na Gwamna ya na da gagarumar gudunmuwa da zai iya bayarwa fiye da haka a hukumance. Akwai maqalar da na gabatar kusan shekaru hudu a baya a babban taro kan almajiranci (Almajiri Summit) a Arewa House, inda a ciki baya ga bibiyar tarihin almajiranci tun daga lokacin Manzo har zuwan turawa, na bayar da shawarwarin hanyoyi na zahiri da za'a iya gyarawa da amfanar da harkar maimakon ta ci gaba da zama nauyi ga al'umma.
1. Ta fannin shari'a gwamnati na iya amfani da majalisa ta yi doka don hana Yara masu karancin shekaru zuwa almajiranci. Idan aka tsaida shekaru sai akalla 12 zuwa sama za a iya tura Almajiri karatu, kuma kada yaro ya wuce jiharsa, nan take ka zabge kashi 50% ko fiye da haka na masu bara.
2. Gwamnati ta gyara firamare yadda Yara zasu iya samun karatu ingantacce kyauta.
3. Kirkirar makarantun tsangayu, kamar yadda Jonathan ya yi, a basu kulawa yadda almajirai kafin kammalawa sun iya sana'o'i da zasu dogara da kansu, kuma tsangayun zasu zama hanyar samawa al'ummar da suke ciki ababen bukatu cikin sauki (sabulu, mai, pure water, dinki, takalma, jakunkuna da sana'o'i iri-iri, noman Rani etc), yadda zasu zama wani manufacturing hub kenan. A cikin wannan sati Kano ta kaddamar da aikin sake Gina majalisar jihar akan naira biliyan 40. Kanawa ba sa bukatar wannan aiki kuma idan za'a saka wannan kudi a aikin gina tsangayu, ana iya samar da tsangayu biyu a kowacce local government (88 kenan) akan Naira miliyan 450 wadda zata dauki almajirai 500 duk tsangaya. Kun ga za a kwashe almajirai dubu 44 kenan daga titi a samar musu wajen kwana da abin sana'a.
Sannan masu hannu da shuni su assasa gina gidajen marayu wadanda su ma za'a koyar da sana'o'i, da assasa yin waqafin gidajen kwana na baki ko wadanda ba su da wuraren kwana.
A lokacin COVID babban Attajirinmu, Abdussamad Rabiu ya bada katafaren rukunin ginin ofisoshinsa a kan Court Road don killace masu COVID, amma wajen na nan har yanzu a yashe ba mai amfanarsa tsawon wadannan shekaru. Me zai hana Gwamna ya roki Abdussamad ya bada wajen ga Gwamnati ta saka gadajen kwana da bude azuzuwa a ciki a rika saka irin wadannan Yara da Gwamna ya samo guda biyu, maimakon wajen yayi ta zama a banza ba mai morarsa?
Kwanan baya a wajen taron kaddamar da littafin IBB, Aliko Dangote, ya sayi littafin na biliyan 8, shi kuma Abdussamad ya sayi na biliyan 5, a junansu sun yiwa IBB cinikin biliyan 13 kenan, wanda ba ya bukatarsu. Me zai hana su biyun su yi wata gidauniya irin haka domin gina gidajen marayu da tsangayu na zamani domin samawa almajirai sana'oi tare da samarwa al'ummomi kayan bukatu? Idan suka samar da irin wadannan tsangayu mutum nawa zasu sami ayyukan yi kama daga koyo da koyarwa da samar da wani manufacturing base ga al'ummar da aka yi tsangayar a wajen? Ta haka fa China ta mamaye manufacturing a Duniya. Shi yawan jama'a alheri ne matukar akwai shugabanci mai kishin al'ummar da zai tallafawa mutanenta su zama masu dogaro da kansu. Almajiranmu, mu na iya mayar da su hanya ta manufacturing din ababen bukatu a kowacce local government, yadda maimakon zama nauyi a kan al'umma sai su zama abin dogaron al'umma.
Ina ganin kalubalen Gwamna ke nan a yanzu, na bin irin wadannan hanyoyin domin magance matsalar bara, kwanan titi da rashin ayyukan yi. Ya na da damar da a yanzu zai iya zunguro wadannan hanyoyin domin ganin an sami canji na zahiri a kasa wanda zai habaka tattalin arzikin jihar Kano. Ba tsinto Yara guda biyu a yi ta hoto da su ana yadawa ba, domin Rana ita yau iwar haka, wani zancen ake ba wannan ba. Lokaci a kullum kurewa ya ke yi mana, kuma alherin da muka yi tsakani da Allah, shi kadai ne abu me dorewa da za mu yi alfahari da shi wata Rana.
Gwamnatin tarayya a nata kokarin ta kafa hukumar Almajiri Commission, kuma Dan Kano ne Chairman a yanzu. Wace irin alaka gwamnatocin Kano da Tarayya su ka yi don morar wannan hukumar ganin yadda Kano ke kan gaba a yawan almajirai?
Kamar yadda bahaushe ya ce "Da, na kowa ne" abin nufi shine dole kowane Uba ya dauki nauyin abinda ya haifa domin shi Allah zai fara tambaya. Gwamnati kuma dole ta dauki nauyin ilimintar da al'ummarta da sama musu ayyuka. Su kuma Attajirai wajibi zakkarsu da tallafinsu ya karkata ga masu rauni a al'umma (Kuma ba wanda ya ke da raunin almajirai a yau), ba su riki ayyukan riya ba, sannan ita kuma al'umma ta tashi tsaye wajen tarbiya da taimakon juna daidai gwargwado. Ta haka, za a iya fara diffusing din bom din yawan jama'a da Arewa ke tarawa kanta. Bom din da tuni ya fara fashewa ya na jeho mana Fulani Yan ta'adda, Yan Boko Haram da kidnappers. Wa ya san me zai zo nan gaba idan ba'a dauki kyakkyawan mataki ba? Allah ya kyauta.
Comments
Post a Comment
Northern Nigeria Perspective is welcoming all comments, observations or views. The use of foul/vulgar language, pornographic materials and such other inappropriate comments are not allowed