Jagorancin Mace a Tarihin Addinin Musulunci Ta Umar Ardo, Ph.D
°Phd. Umar Ardo delivering a speech during a function.
Jagorancin Mace a Tarihin Addinin Musulunci
Ta Umar Ardo, Ph.D
Ni ba malamin fikihu ko malam na ilimin addinin Musulunci ba ne, amma ni malamin tarihin duniya ne. Saboda haka, ba zan yi magana da cikakken ilimin addini kan matsayin addinin Musulunci game da jagorancin mata ba - wannan sai a bar wa malamai! Amma a matsayina na Musulmi, na san kadan daga abin da Musulunci ya ce game da mace da mulki a kan al’umma. Banda abin da *Al-Qur’ani Mai Girma* da *Hadisan Annabi (SAW)* suka fada, akwai kuma abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci da suka kara fayyace matsayin Musulunci kan jagorancin mata. Saboda haka, a matsayin mai binciken tarihi - musamman tarihin Musulunci - zan yi bayani bisa abin da tarihi ya nuna game da wannan batu.
1. Ba da shawara da wakilanci daban, jagoranci kuma daban. A tarihin Musulunci, mace tana iya bada shawara ko wakilanci, amma ba ta da ikon jagoranci. Abin da *Qur’ani* da *Hadisi* suka bayyana a kai, kamar yadda na ce a baya, na bar wa malamai su yi bayani. Amma ga abin da tarihi ya nuna - ga wasu ‘yan misalai.
2. A farkon Musulunci, babbar mai ba *Annabi (SAW)* shawara ita ce matarsa Khadijah. Daga baya ma *Annabi (SAW)* ya nemi shawara daga Ummu Salamah (r.a.) lokacin da wasu daga cikin sahabbansa suka nuna adawa da sa hannunsa a Yarjejeniyar Hudaibiyyah, wadda a ganin su bai kamata ya yarda da ita ba. A fannin wakilanci ma, tarihi ya nuna cewa mata sun taka rawa. Misali, Khalifa Umar ibn al-Khattab (r.a.) ya nada mata kamar Al-Shifa bint Abdullah da Samra bint Naik al-Asadiyyah a matsayin masu lura da kasuwanni a Madina da Makkah don tabbatar da cewa ana yin kasuwanci kamar yadda shari’a ta tanada.
3. Amma a fannin jagoranci, malamai sun bayyana cewa Musulunci ya hana mace ta zama liman, ma’ana Musulunci ya hana mace jagoranci, domin liman shi ne jagora. Da Musulunci yana so mace ta yi jagoranci, da ba zai hana ta limanci ba. Haka kuma, tarihi ya nuna cewa babu mace ko guda daya daga cikin annabawan Allah. Da *Allah (SWT)* yana so mace ta yi mulki, da a cikin annabawan da ya aiko - guda 124,000 - da ya sa a kalla mace guda daya. Amma *Allah* bai yi hakan ba.
4. A tarihin sarakunan Musulmi, tun daga zamanin *Annabi (SAW)* zuwa Abubakar, Umar, Usman, Ali, zuwa Daular Ummayad, Abbasiyya, Turkiya, Usmaniyya, Almoravid, har zuwa yanzu da Sultan Sa’ad na Daular Sakkwato - babu mace da ta taba zama shugabar Musulmi. *Allah (SWT)* bai halatta hakan ba. Haka ma, idan muka duba lokacin da *Annabi (SAW)* ya rasu, ya bar ‘yar sa Fatimah. To me ya sa Fatimah ba ta gaje shi ba? Fatimah ma ta fito ta nemi gadon mahaifinta, ba annabci ba, amma jagoranci - kamar yadda Ishaku, Yakubu da Sulemanu suka gaji ubanninsu. Amma an hana ta, kuma ba ta zama shugaba ba.
5. Haka kuma, me ya faru a Yaƙin Jamal (Yaƙin Rakumi) a Basra a shekara ta 36 bayan hijira, lokacin da A’isha, matar *Annabi (SAW),* ta jagoranci sojoji? An ci ta da yaƙi, aka kama sojojinta. Idan hakan zai iya faruwa da Fatimah ‘yar Annabi da A’isha matar Annabi, to wace mace ce za ta iya cewa za ta zama shugabar al’umma? Ba wai mata ba su taba shiga yaƙi ba a tarihin Musulunci - a’a, sun shiga. Misali, Nusaybah bint Ka’ab ta yi jajircewa a gefen *Annabi (SAW)* a yaƙin Uhud da Hunayn, har *Annabi (SAW)* ya yaba da jarumtar ta. Haka kuma a zamanin Mu’awiyah ibn Abi Sufyan, an ga jarumtar Umm Hiram a fagen daga. Amma waɗannan matan ba su jagoranci yaƙin da suka shiga ba.
6. Wani abin la’akari kuma shine akwai wata mace guda daya tilo Musulma da ta yi mulki a Masar mai suna Shajar al-Durr, ma’ana “Itacen Lu’ulu’u”. Ta zama Sarauniyar Masar a shekara ta 1250, wanda ya kawo sauyin mulki daga Daular Ayyubawa zuwa zamanin Mamlukai. Ta yi hakane a lokacin da mijinta, Sarkin Masar, yake cikin mummunan rashin lafiya kuma daga baya ya rasu yayin Yaƙin Salibi na Bakwai. Shajar al-Durr ta ɓoye labarin mutuwarsa domin ta kare tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar. Harma ta jagoranci dakarun Masar ga nasara, inda suka doke sojojin Salibi kuma suka kama Sarki Louis na IX na Faransa. Ganin haka, bayan rasuwar mijinta, manyan shugabannin Mamlukai da jami’an gwamnati suka amince da ita ta zama mai mulkin ƙasa. Amman al’umma su ka yi asha suka ƙi mulkinta a matsayin mace. Don hakan karagar mulkin ta bai daɗe ba - kusan kwanaki 80 kacal - saboda adawa mai ƙarfi daga shugabannin addini da Halifan Abbasiyya na Bagadaza, wanda ya aika da saƙon suka yana tambaya ko a Masar babu namiji da ya cancanci mulki.
7. Domin ta sasanta lamarin da masu adawa, Shajar al-Durr ta auri janar ɗin Mamlukai, Izz al-Din Aybak, ta kuma miƙa masa mulki, amma ta ci gaba da riƙe da ƙarfin iko a bayan fage. Daga baya, an kashe ta a shekara ta 1257.
8. A zamanin nan ma, me ya faru lokacin da Amurka, Ingila da Faransa suka tilasta wa Musulman Pakistan su amince da Benazir Bhutto, ‘yar tsohon Firayim Minista Ali Bhutto, a matsayin shugabar ƙasar, duk da fatawar da malamai suka bayar cewa hakan ya sabawa sharuɗɗan addinin Musulunci? Pakistan ta fada cikin rikici, sannan Benazir Bhutto kanta aka kashe ta a titi.
9. Dukkan waɗannan misalai darussa ne ga al’ummar Musulmi masu ilimi, basira da fahimta. Lamarin ya bayyana a fili ga masu hankali.
10. Saboda haka, duk wani fassara da za a yi wa ayoyin *Qur’ani* ko *Hadisi* da bai yi daidai da abin da tarihi ya tabbatar ba - daga *Annabi (SAW)* har zuwa Daular Usmaniyya - wannan fassarar ba za ta zama gaskiya ba. Mutane za su iya cewa ko yin abin da zuciyarsu ke so saboda jahilci ko son rai, amma hakan ba abin mamaki ba ne.
11. Tarihin addinin Musulunci ya riga ya shimfiɗa matsayin mace a jagoranci. Abin da ya rage yanzu shi ne mu tantance: mu bi ko mu ƙi bi. Idan demokuradiyyar zamani za ta yi fatali da hujjojin Musulunci da tarihin addini, to mu saurara mu gani. Mun bayyana hujjojin kamar yadda tarihi ya nuna. Masu bin hujjar Musulunci su bi, masu bin hujjar demokuradiyya ma su bi. Kowa ya yi bisa fahimtarsa da ra’ayinsa. Amma mu sani abubuwa guda biyu:
12. Na farko, babu abin da zamani zai kawo - kamar demokuradiyya ko kundin tsarin mulki - da zai iya rushe hujjar Musulunci ga Musulmi; Na biyu, komai a ƙarshe yana da sakamakonsa.
13. Hazaa wassalam!
Comments
Post a Comment
Northern Nigeria Perspective is welcoming all comments, observations or views. The use of foul/vulgar language, pornographic materials and such other inappropriate comments are not allowed