KURA-KURAI GOMA NA KIMIYYA A QUR’ANI...IN JI MULHIDAIAli Abubakar Sadiq
A baya bayan nan Mulhidai, Riddaddu da makiya Musulunci sun shigo da wata sabuwar hanya ta sukar addinin musulunci, musamman a kasashen yamma, ta amfani da cewa akwai tarin kura-kurai na kimiyya a cikinsa. Na sha gwagwarmaya da irin wadannan mutane a dandalin Quora inda na kalubalanci duk wani mai wannan da’awar ya kawo duk wani abu da yake tsammani na kimiyya ne wanda ya ci karo, ko ya sha banban da Qur’ani. Dalili na kuwa bai wuce cewa na yi imani da cewa Allah dai shine wanda ya yi duk wata halitta, kuma a tsari irin na kimiyya ya yi halittunsa, sannan shine wanda ya saukar da Qur’ani, don haka duk wanda ya ce akwai karo daga wadannan bangarori guda biyu, to tabbas bai wuce ko dai ba shi da ilimin Qur’ani yadda ya kamata, ko kuma ba shi da ilimin kimiyya cikakke.
Abokan muhawara ta sun kalubalance ni da kawo tambayoyi guda goma da su ka jibanci kimiyya a Qur’ani wadanda su ka hada da;
1.Samar da maniyya a jikin dan Adam (Sperm factory)
2. Halittar mutum daga gudan jini (Embryology)
3. Tarihin asalin samuwar halittu (Evolution)
4. Sama a matsayin rumfa (Earth atmosphere)
5.Tsaunuka a matsayin turaku da ke rike kasa (Mountains as pegs)
6. Adadin duniya guda nawa (Earth layers)
7. Zagayen Rana (Solar orbit)
8. Wata a matsayin haske (Lunar light)
9. Shingen da ya raba tekuna (Sea barrier)
10. Faduwar Rana (Sunset)
To bari mu bisu daya-da-daya.
1. SAMAR DA MANIYYI – Bayanin Qur’ani na inda ake samar da maniyya a jikin Dan Adam ya sami kalubalen cewa ya ci karo da na kimiyya. Allah ya ce a cikin Suratul Darik
Q86:6-7 “An halitta shi daga wani ruwa mai tunkudar juna...ya na fita daga tsakanin tsatso da karankarmar kirji”
Sai su ka yi wuf su ka ce “Ayya...Qur’ani ya kwafsa a kimiyance a nan, saboda maniyyi daga cikin yayan gwaiwa ake samar da shi (testes)”. To ku dan dakata mana. Allah ya yi amfani da kalmar larabci "Sulbi" wadda ke nufin tsatso wadda ita dai Allah ya yi amfani da irinta cikin Suratul Ma’ida a aya ta 23 wato “Aslabikum” wadda ke bayanin cewa “Da matan yayanku wadanda su ke daga tsatsonku” a larabci da turanci Kalmar na nufin “Loins” wato daga kasan kirji zuwa yan maraina. To, menene ya ci karo da kimiyya da ke cewa maniyyi ana samar da shi a maraina?
3. HALITTA DAGA GUDAN JINI – Shi ma wannan bayani na Qur’ani ya gamu da suka. Allah ya ce cikin Suratul Alaq
Q96:2 “Ya halitta mutum daga gudan jini”
Allah ya kira surar gaba dayanta da “Gudan jini” wato Alaq, kalmar da ba ka iya fahimtarta yadda ya kamata sai ka san tsarin kimiyya na yadda Allah ke halitta mutum a cikin ciki. Kafin kimiyya ta gano yadda tsarin ya ke, har zuwa kusan karni na 18 ana daukar cewa jariri na farawa ne a dan mitsitsi da duk sifofinsa cif, kafin ya girma a hankali ya isa haihuwa. Amma Allah sama da shekaru 1400 ya yi bayanin yadda yanayin ya ke tun daga daukar ciki zuwa haihuwa. Wannan bayani ya zo a warwatse cikin Qur’ani, bari mu biyo shi tun asalinsa. Allah ya fara da gaya mana cikin suratul Yasin cewa:
Q36:36 "Tsarki ya tabbata ga wanda ya halitta nau'ika na namiji da mace, dukkansu daga abinda kasa ke tsirarwa, Kuma daga (su) kansu, Kuma daga abinda ba su sani ba"
Hikimar hakan shine domin Allah ya tabbatarwa dukkan wata halitta buwayarsa cewa shine kadai tilo. Amma duk wata halitta, mai rai ko maras rai ta bi tsarin cewa ta na da kishiya, shi kadai ne ba shi da kishiya. Halitta mara rai dukkanta daga kwayar zarra take (Atom) wanda electrons da ke ciki na bin tsarin lantarki mai karbar wuta (+ positive) da mai bada wuta (- negative). Halitta mai rai kuma ko wacce iri, na cikin tsarin kwayar halitta (cell) da ke da sinadarin mace da namiji, hatta halittu masu kwayar halitta daya (asexual), sashen mazakuta ke barbarar ta mace. Akasarin halittu masu rai na samuwa daga wannan tsari na barbarar namiji da mace a daidaikun halittu biyu (sexual). Akwai kuma masu kwayar halitta daya wadanda ke da namijin da mace a halitta guda (Hermaphrodite). To, a tsarin halttar mutum sai Allah ya fara da cewa
Q56:58-59 "Shin kun ga abinda kuke fitarwa na maniyyi…shin ku ne kuka halitta shi ko mu ne masu halittawa?"
Wato matakin halitta na farko shine daga maniyyi na namiji wanda ke shiga cikin mace bayan saduwa. Daga nan sai Allah ya ce
Q86:6-7 “An halitta shi daga wani ruwa mai tunkudar juna”
A kowacce fitar maniyyi daga namiji izuwa jikin mace, akwai kwayoyin halittar mutum (spermatozoa) kama daga miliyan 150 zuwa miliyan 200 a cikin duk millitre daya ta maniyyi na lafiyayyen mutum. Kowanne daya kuma cikin wadannan miliyoyi 200 zai iya samar da mutum. To wannan dandazon shine fa a jikin mace bayan jima'i, sai su kama tsere da rigegeniyar wanne a cikinsu zai iya fasa kwan macen ya zama shine ango? Wato wannan tsere shi Allah ke nufi a wannan aya da ke cewa “Su na tunkudar juna”. Kwayar maniyyin, an suranta ta yadda jikinta ya zama kanta kewayye ne wanda aka lullube da wani sulke-sulke a goshinsu, sai kuma doguwar jela tamkar yadda zaka ga yayan kwadi bayan kyankyasarsu. Jelar ta su kuma kamar ta maciji, ita ke tunkuda su domin iyo cikin gaggawa. A yayin da su ka isa ga kwan mace, sai su kewaye shi su yi masa kuri su yi amfani da wannan sulke na goshinsu wajen samun nasarar fasa wannan kwai. To duk wanda ya riga fara fasa wannan kwai sai ya shige cikinsa. A hikimar Allah, Kwan mace, shine kwayar halitta (Cell) mafi girma cikin kwayoyin halitta a jikin Dan Adam kuma ya ninninka na maniyyi. Hikimar shine idan maniyyi ya shige cikinsa su ka dunkule, shine mataki na samuwar sabon mutum, mace ko namiji (fertilized ovum) don haka ya na bukatar wannan girma domin hadiye maniyyi da samar da sinadari domin rayuwar dan tayi a cikin mahaifa. To da zarar gudan maniyyi ya sami zama wannan ango, gaba dayan sauran miliyoyin kwayoyin maniyyin sai su yi saranda su mika wuyar cewa an kasa su. Sai Allah ya ci gaba da bayani a cikin suratul Insan (Mutum)
Q76:2: "Lallai ne hakika, mu mun halitta mutum daga wani ruwa garwayayye"
Kun ji Kalmar da Allah ya fada “Garwaya” wato ya garwaya kwayar maniyyi da kwan mace lokacin da aka daura wannan aure a cikin mace (Fertilization). Sannan kuma da maniyyi da kwai na macen, kowannesu na dauke da kwayoyin halittar gado (Chromosomes) guda 46 kuma tagwaye ne, wato bibbiyu (haploid). Amma sakamakon wannan gauraya, sai maniyyi ya yago rabin wadannan kwayoyin halittar gadon nasa, wato guda 23 yayinda kwan mace shi ma sai ya yago nasa rabin, 23 sai su gauraya wadannan rabi-rabin yadda idan su ka dunkule kaga sun sake samar da wasu 46 da kowanne mutum ke dauke da su. Wannan ne ya ke sa ake samun gadon sifa (genes) da halayya ta iyaye biyu, mace da namiji a jikin dan su. Bayan wannan gauraya, wane mataki kuma dan tayin zai hau?
Q23:13 "Sannan mu ka sanya shi digon maniyyin a cikin matabbata nutsatstsiya”
Wannan garwayayyen digon maniyyin (fertilized ovum) sai ya bi wani bututu (fallopian tube) ya shiga mahaifa (Uterus) inda zai je ya makale a jikinta (Uterine wall). A nan, dan tayin zai fara rayuwa ya na samun abincin da zai gina jikinsa har zuwa haihuwa. To a nan ne fa shi wannan garwayayyen maniyyi zai fara rabewa, daga daya ya zama biyu, su kuma su zama hudu, hudun su zama takwas, zuwa sha shida, talatin da biyu, haka-haka dai kwayar halittar za ta yi ta ninkawa har sai ya zama daruruwa wanda zai dunkule (blastocyst)
Q23:12 “Kuma lallai ne, hakika mun halitta mutum daga wani tsantsa”
Ya fara zama tsoka (Morula) ke nan da ke dauke da kwayoyin halitta na asali (stem cell) wadanda ke iya samar da duk wani sassa na halittar mutum. Kamar yadda Allah ya ci gaba da bamu bayani a
Q23:14 “Sannan kuma mu ka halitta shi gudan jini”
Sai kuma jijiyoyin jini su karade wannan tsoka da ke dauke da kwayoyin halittar na asali (stem cell) da ke dauke da bayanai (information) da zasu iya zama kowane irin kwayar halitta a jikin mutum kamar su jini, tsoka, kashi, jijiya ko gashi kowannensu. Daga nan kuma sai…
Q23:14 “…Sannan muka halitta gudan jinin tsoka, sannan mu ka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sannan muka tufatar da kasusuwan da wani nama (fata)"
Wato sai ya bi tsarin watanni 9 na cacanzawa a hankali ya na habaka har a sami cikakkiyar surar mutum kafin haihuwar.
Abu na gaba mahimmi a dan tayin shine banbance yadda halittar za ta zama, wato mace ko namiji? Sai Allah ya ce mana
Q92:3 "Da sirrin da ya halitta namiji da mace"
Wato a cikin kwayoyin halittar gado da na ambata a baya, yan tagwayen nan 23 (da idan sun hade na mace da na namiji ke samar da kwayoyin chromosomes 46 na sabuwar halitta) to a tagwayen na 23 na mace, zaka samu duk biyun dogwaye ne amma a na namiji guda daya dogo ne dayan kuma gajere. To a wajen waccan garwaya da Allah ya ambata (Fertilization) idan dogo na mace ya hadu da dogo na namiji (wato su ka zama duk dogwaye ke nan) sai abinda za’a haifa ya zama namiji. Idan kuma na mace dogo ya hadu da na namiji gajere (wato dogo da gajere su ka hade) sai jaririyar ta zama mace. Kafin kimiyya ta habaka, ana tsammanin cewa gado a cikin jini ya ke tun zamanin su Aristotle shekaru 2500 da su ka gabata. Amma yanzu an gane cewa jini aikinsa daban. Akwai kwayoyin halitta na jini (Blood cells) kala uku, wato jajaye (red blood cell) wadanda ke baiwa jinin launinsa. Su ne ke dakon abinci, iska, da gubar da ake fitarwa daga jiki. Sai farare (White blood cell) wadanda aikinsu shine yakar kwayoyin cututtuka da kuma na karshen da ake kira platelets wadanda aikinsu shine daskarar da jini idan an ji ciwo kada jinin jiki ya tsiyaye. Bayanin karshe shine cikin suratul Hajj da Allah ke cewa
Q22:5 “"Lallai ne mu, mun halitta ku daga turbaya, sannan kuma daga gudan jinni, sannan kuma daga tsoka wadda ake halittawa da wadda ba’a halittawa"
Me Allah ke nunawa anan da cewa tsoka da ake halittawa da wadda ba’a halittawa? Wato da farko ya dauko asalin samuwar halitta daga turbaya ko mu ce sinadarai wadanda da su aka gina duk wani jiki Mai Rai (Carbon, Nitrogen, Oxygen, Hydrogen, Phosphorus da Sulfur) Sannan daga gudan jini da tsoka wanda bayani ya gabata. Sai kuma tsokar da ake halittawa da wadda ba’a halittawa. Wannan na bayani ne yadda surar dan tayi ke caccanzawa tun daga garwayayyen maniyi da kwan mace wanda a farko ke kamanni da talibanban, wato yayan kwadi. Sannan tsagun numfashi (Gill arches) irin na kifi su bayyana. Tsokokin a jejjera su kamar na dabbobin da can masu kashin baya kafin a juya su zuwa kwanji irin na dan Adam. Sannan jela ke fitowa a daidai kugu irin ta birai amma kafin haihuwa sai ta zuke ta koma. Duk wadannan siffofi na kwado, kifi, dabbobi masu kashin baya da biri ai kun ga a karshen halittar jariri duk bacewa su ke yi, shi ne abinda Allah ke nufi da wadanda ba’a halittawa. Amma Allah ya kawo su domin warwarar tarihin halittarmu a wannan duniya yadda muka biyo kafin zama mutum. Sai kuma a karshen karshe na wanna tsari Allah ya rufe da cewa
Q23:14 "Sannan muka halitta shi gudan jini, sannan mu ka halitta gudan jinin tsoka, sannan muka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sannan mu ka tufatar da kasusuwan da wani nama (fata), SANNAN MUKA KAGA SHI, WATA HALITTA TA DABAN”
Wato halitta da ta faro daga digon maniyya kwaya daya ta zama tiriliyoyin kwayoyin halitta (cells) da su ka samar da sassa na jikinmu (organs) da yadda ta bi matakai daban daban yadda kafin a sami cikakkiyar sura ta mutum, wadanda a matakai daban daban idan aka fito maka da dan tayi aka ce mutum ne ba za ka yarda ba, abinda ke jaddada tarihinmu a baya (evolutionary past). A karshe duk a ka yi watsi da wadannan siffofi, aka kagi wata sura ta daban, wato ta mutum wadda ita ce ake haihowa kunshe da tiriliyoyin kwayoyin halitta. Wato Dan Adam dandazo ne na tiriliyoyin kwayoyin halitta, kuma ya faro ne daga kwayar halitta guda tamkar yadda halitta mai rai ta faro ta watsu ta fantsama. Tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta gwani, masani.
Don haka masu cewa Qurani ya yi kuskure wajen ambata halitta mutum da ga gudan jini, sun yanko wani sashen ne ba tare da sanin cewa Qurani ya kawo abin daki-daki tun daga farkon samuwar ciki har zuwa haihuwa ba, tun shekaru 1400 da su ka gabata, alhali kimiyyar kanta bata fara gane yadda abin ya ke ba sai a shekaru kasa da 200 da su ka gabata.
Mu hadu a kashi na biyu domin dorawa daga inda mu ka tsaya.
Comments
Post a Comment
Northern Nigeria Perspective is welcoming all comments, observations or views. The use of foul/vulgar language, pornographic materials and such other inappropriate comments are not allowed