SHEKARU BIYUN TINUBU, GABA A KA CI KO BAYA?Ali Abubakar Sadiq
Hakika a shekaru biyun nan, tabbas akwai abubuwa da su ka sami gagarumin ci gaba, yadda a tarihin kasar nan ba'a taba ganin irinsa ba. Haka kuma a daya hannun, abubuwa da dama sun yi koma bayan da ba'a taba ganin irinsa ba.
Bari mu fara da ci bayan da aka samu. Tashin farko dai, a 2023 tattalin arzikin Najeriya shine mafi karfi a fadin Africa, yayin da Egypt, South Africa da Algeria ke biye da mu. Amma daga ranar da aka rantsar da Tinubu kuma ya karya kumallo da cewar an cire tallafin mai, nan take karfin tattalin arzikin Najeriya ya fara zamiya har zuwa yanzu, yadda a karshen shekarar 2024 sai gashi mun koma na hudu a bayan South Africa, Egypt da Algeria.
A watan Mayu 2023 Tinubu ya sami Dollar a Naira 460 amma a yau da nake wannan rubutu ta ninka kusan sau hudu, wato Naira 1571. Shi ma man fetur yayi tashin gwaron zabi kamar Dollar inda ya ninka kusan hudu a yau, wato daga Naira 254 zuwa Naira 950 akalla.
Bayan cire tallafin, gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa jama'ar kasa su yi hakuri domin wasu Yan kulob (Subsidy Cabal) ne kadai ke morar tallafi ba Yan kasa ba, don haka za'a rika samun rarar Naira biliyan 500 duk wata wadda za'a karkato ga yiwa talakawa aiki. Musamman samar da sufuri da karin albashi da samar da jari ga kananan Yan kasuwa da masana'antu da sauransu. Wannan kudade sun fara shiga lalitar gwamnatin tarayya daga watan June na 2023. Wato idan ka lissafa akan yadda aka kiyasta, zuwa yanzu (May 2025), gwamnati ta kalmashe naira Tiriliyan 12 daga kudin rarar na janye tallafin mai. To abin tambaya mai karatu, cikin duk abubuwan da aka lissafa za'a yi mana, wanne ne ya tabbata? Idan babu, to ina kudaden?
A nan ne zamu koma kan maganarmu ta farko cewa akwai sassa da su ka samu ci gaba da ba'a taba ganin irinsa ba. Cikin wadannan sassa shine; duk wanda ke bibiyar yadda ake kasaftawa da rarraba kudaden FAAC, zai ga inda kudade, ba kawai na cire tallafin ba, har da na haraji da basussuka da ake ciyowa suka yi habakar da a tarihin Najeriya ba'a taba samun lokaci da gwamnatin Tarayya, Jihohi da kananan hukumomi ke samun kudade ba kamar a wannan gwamnati.
Cikin watan Mayu na 2025 dinnan, Babban Bankin Duniya ya fitar da wani rahota inda ya zargi kamfanin NNPCL cewa basu mika kaso 50% na kudaden da aka janye na tallafi ba. Wannan shi ma wani sabon ci gaba ne da aka samu. Sannan a baya munga yadda aka hankadawa Yan majalisar dokoki miliyoyin Nairori a matsayin albashi da alawus wanda takwarorinsu na baya basu taba samu ba. Lokacin da Tinubu ya karbi Mulki a 2023, talauci a Najeriya ya riga ya zama ruwan dare sakamakon karya tattalin arziki da Buhari ya yi, yadda muka karbi kambun cibiyar talauci a duniya da kaso 38.9%, wato kimanin mutane miliyan 87. Amma fa a kasa da shekaru biyu na mulkin Tinubu, wato zuwa karshen 2024, sai ga shi talauci ya karu da kaso 54% wato kimanin mutane miliyan 106. Wato a wannan kankanen lokaci na Tinubu ya sake jefa mutane kusan miliyan 20 cikin talauci sakamakon tsare-tsarensa na tattalin arziki.
A takaice ya bayyane ya ke kururu cewa hakika kasar Najeriya ta sami arziki gagarumi daga 2023 zuwa 2025 amma daga aljihun talaka aka kwakwulewa ake mikawa Yan siyasa da mahukunta kawai, ana ta dada nutsar da talakawa cikin talauci. Domin a 2023 Najeriya ta sami kudaden Mai na Tiriliyan 8 amma a 2024 kadai, ta sami Tiriliyan 50, yayin da ake tsammanin Tiriliyan 84 zuwa karshen 2025. Idan ka hada kudaden 2023-2024 kadai, an sami jumillar Tiriliyan 134 wato kusan dala biliyan $90 kenan. Don girman Allah ina wadannan kudade a kasa? Kuma kada mu manta cewa a shekaru takwas na Buhari, Najeriya ta sami kimanin dala biliyan $312 tsakanin kudaden Mai da basuka. Yayin da wannan gwamnati zuwa 2024 ta ci nata bashin na dala biliyan 31 a shekarar farko. Sannan masana na hasashen cewa za'a ci bashin jumillar dala biliyan $60 kafin karshen 2025, wanda alamu su ka tabbatar domin a daf da bikin cika shekaru biyu a kan mulki, Tinubu ya sake mikawa majalisa bukatar cin bashin wasu dala biliyan $21.5. Jumlatan idan ka hada wadannan kudade na Mai da bashi, a shekaru goma na mulkin APC (2015-2025) sun kai dala biliyan $462.
Ta yaya kasar da ta sami wannan kudade da ba'a taba ganin irinsu ba a tarihinta kuma a ce al'ummarta na cikin yunwa da talauci?
Shi yasa kada mu rika mamakin yadda gwamnoni APC su ka goyawa tazarcen Tinubu baya, har wasu gwamnonin da Yan majalisu ke turmutsitsin komawa APC. A nan Arewa munga yadda masu fada a ji a siyasa, wato gwamnoni da Sarakuna su ka yiwa Tinubu mubayi'a. Kada mu manta da cewar shi tarihi kullum ya kan maimaita kansa ne. A 2014 haka Yan siyasa da masu fada a ji su ka yi ta yi wa Jonathan mubayi'a, amma da zabe ya zo ya aka kaya? Alamu na nuna cewa Tinubu shi ma zai iya fuskantar haka matukar yan adawa su ka iya dinke kansu waje daya. Domin a zaben 2023 su suka kada kansu domin su na da kuri'a kusan miliyan 14 amma Tinubu ya kayar da su da kuri'a miliyan 8.
Ita kanta gwamnati ta gane wannan barazana ta Yan adawa shi yasa babban abinda ta saka gana shine murkushe adawa. A yanzu kusan ace PDP ta mutu murus saboda APC ta hadiye ta. Gwamnoninta 5 sun sahalewa Tinubu tazarce. Sannan an jiyo wata jita-jita cewa Ganduje ya bada shawarar a manta da matasa a rike shugabanni siyasa, Wike na cewa yan Arewa mayunwata ne, da an zuba mana tsaba za mu bi mu karba mu kada kuri'a.
To yanzu dai ya ragewa Yan Najeriya su yankewa kansu hukunci a kan wannan gwamnati, shin ci gaba aka samu ko ci-baya? Shin talaka ba shi da tasiri idan aka rike Yan siyasa? Ko kuma za mu ci gaba da zama mabarata a bamu taliya a ci zabe? Shin yan adawa masu kuri'a miliyan 14, zasu sake yin kasassabar barin gwamnati me kuri'a miliyan 8 ta sake kayar da su? Lokaci kadai zai tabbatar da hakan ko akasin haka. Sannan dabara ta ragewa Mai shiga rijiya.
Comments
Post a Comment
Northern Nigeria Perspective is welcoming all comments, observations or views. The use of foul/vulgar language, pornographic materials and such other inappropriate comments are not allowed